Cin Zarafin Naira: Kungiyar NCSO Ta Nemi EFCC Ta Kama Dan Takarar Gwamnan APC

Publish date: 2024-07-23

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Edo - 'Dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo na watan Satumba mai zuwa, Monday Okpebolo, na iya fuskantar hukuncin daurin watanni shida a gidan yari.

Wannan kuwa, a cewar gamayyar kungiyoyin farar hula a karkashin inuwar kungiyar farar hula ta Najeriya (NCSO) zai iya faruwa ne saboda Okpebolo ya ci zarafin Naira.

Kara karanta wannan

Kanun jaridu: Gwamnati za ta yi wa mutane miliyan 1.9 rajistar sana'ar PoS

'Dan takaran APC ya karya dokar CBN?

Punch ta ruwaito kungiyar NCSO ta zargi dan takarar gwamnan da karya dokar Babban Bankin Najeriya ta 2007 bayan da aka ganshi yana watsa kudi a wajen biki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta kai karar Okpebholo ne ga hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) a wata kara mai dauke da kwanan wata 2 ga watan Mayun 2024.

Shugaban kungiyar na kasa, Victor Kalu, da sakatarensa na kasa, Ali Abacha ne suka sanya hannu kan takardar.

NCSO ta nemi EFCC ta binciki bidiyo

Kungiyar ta ce:

"Abin takaici ne yadda wasu fitattun mutane ciki har da 'yan majalisa da 'yan takarar gwamna suka karya wannan dokar ta CBN."

A yayin da ta ke yabawa hukumar ta EFCC kan kokarin yaki da masu cin zarafin Naira, kungiyar ta bukaci hukumar da ta gaggauta kama duk wanda aka kama ya karya doka.

Kara karanta wannan

Hukumar UBEC za ta yi horo na musamman ga malamai 1480

Ta yi kira ga hukumar EFCC da sauran jami’an tsaro da su binciki “bidiyon da ke nuna Sanata Monday Okpebolo yana cin zarafi da lalata takardar Naira.”

NCSO ta yi barazanar yin zanga-zanga

Kungiyar ta kara da cewa ya kamata a tuhumi Okpebolo a matsayinsa na wakilin jama’a, jaridar SaharaReporters ta ruwaito wannan.

Sai dai kungiyar ta yi gargadin cewa rashin daukar mataki kan faifan bidiyon Okpebolo zai sa kungiyar ta kara daukaka kara zuwa gaba.

Shugabannin kungiyar sun yi barazanar tattara 'ya 'yansu, magoya bayansu, da masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya domin gudanar da zanga-zangar lumana kan EFCC ma damar ba ta dauki mataki ba.

An gurfanar da 'barayin biredi' a kotu

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda wani kamfanin abinci a jihar Oyo ya gurfanar da ma'aikatansa biyu kan zargin sun satar masa biredi guda biyu.

Kamfanin ya shaidawa kotun cewa ma'aikatan sun hada baki ne suka saci biredin da kudinsu ya kai N2,600, zargin da ma'aikatan suka karyata.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbn51fZRmmqKmXa%2Bus63FoqVmppGev6J5yq6loKGplr9uusKspmaskWK7prnIZpyfm5NiwaJ5ypqkmmWUlrtuwMCkmKuZomK0uK3Mp5inZZGlsHA%3D