Rikicin APC a Kano: Kotu ta Hana Kama Wadanda su ka Kori Ganduje a Jam'iyya
- Wata babbar kotu ta haramtawa jami'an rundunar yan sandan daga gayyata ko kama wadanda su ka kori shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje daga jam'iyyar
- Hukuncin na zuwa ne bayan Haladu Mai Gwanjo da wasu mutum 10 da suka jagorancin korar Abdulllahi Ganduje daga mazabarsa sun shigar da kara kotu
- Sun nemi kotu ta dakatar da jami'an tsaro daga nemansu ko kama su kamar yadda rahotanni ke cewa jami'an tsaro na farin kaya sun fara nemansu ruwa a jallo
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano- Wata babbar kotu da ke zamanta a Kano ta haramtawa Sufeto Janar na 'yan sanda da Mataimakin Sufeto Janar na da ke shiyya ta daya a Kano da Kwamishinan 'yan sandan jihar daga kokarin kamawa ko gayyatar wadanda su ka kori tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje daga APC.
Ya kamata Najeriya ta jagoranci kasashen Afrika a girman tattalin arziki, Shehu Sani
A dambarwar da ke ci gaba da ruruwa a APC Kano, wani tsagi na jam'iyyar ya sallame tsohon Gwamnan daga jam'iyyar baki daya.
Tun bayan korar Abdullahi Umar Gandujen ne uwar jam'iyya ta nemi jami'an tsaro su kama wadanda su ka yi korar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma tuni tsagin su Haladu Gwanjo ya nemi kotu ta shiga tsakani, kamar yadda Daily Trust ta wallafa rahoton.
APC: Kotu ta ba Mai Gwanjo kariya
A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, Mai Shari'a Yusuf Ubale Muhammad ya takawa majalisar gudanarwa na APC da jam'iyyar a matakin jiha burki.
Sannan an dakatar da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje daga amfani da jami'an tsaro wajen kamowa ko gayyatar wadanda su ka kore shi har sai kotu ta yanke hukunci kan karar.
A rahoton da Channels Television ta fitar, wasu 'yan jam'iyyar APC a mazabar Ganduje da su ka hada da Haladu Mai Gwanjo, Jafar Adamu da wasu mutum goma sun shigar da kara.
'Yan sanda sun kwamushe mutum 3 da ke ikrarin su jami'an EFCC ne
Laminu Sani Barguma da wasunsa su na rokon kotu ta hana take musu hakkinsu na 'yan Adam.
Hukuncin ya diga aya ga nemansu ruwa a jallo da jami'an tsaron farin kaya na DSS ke yi bisa umarnin shugaban jam'iyyar APC na jiha, Abdullahi Abbas.
"Ba zan jijjigu ba!" - Ganduje
Mun ruwaito muku a baya cewa Abdullahi Umar Ganduje, tsohon Gwamnan Kano kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa ya ce babu abun da zai taba kujerarsa duk da rikici da ya kunno kai a jam'iyyarsa.
Ganduje na wannan furuci ne a sa'ilin da ake shirin gurfanar da shi gaban kotu kan tuhume-tuhumen da suka jibanci cin hanci da rashawa.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ6fJZwamaqmaC2pLXNZpipm12WeqytzahkpKekqnq1rYyhmKeZXaCurq2MsJidmZ6Zrm6%2F1GaimmWbpL%2BqecaapZ2tmpp8